Featured post

Sean Dampte UK based singer, drops new track,‘Energy’

Wednesday 28 February 2018

Kishi: Wani magidanci ya gamu da fushin uwardakin shi, ta watsa masa ruwan batiri a gaba

Ta watsa ma mijinta ruwan batiri a gaba bisa dalilin yi ma aminiyarta ciki

Ta zuba masa ruwan batiri a gaban shi yayin da yake bacci wanda yayi sanadiyar mutuwar shi bisa dalilin yi ma aminiyarta ciki

Wani magidanci a jihar Kaduna ya gamu da fushin uwardakin shi inda ta kwararo masa ruwan batiri yayin da yake bacci bisa dalilin yi ma aminiyar ta ciki.

Uwardakin ta aikata hakan ne bayan ta tarbe mijinta hannu biyu bayan dawowar shi daga wani dan gajeren tafiya da yayi. Cikin rarrashi ita da mijin nata sunyi kwanciyar ma'aurata sai dai bayan kwantatawan da ta nuna mashi can cikin dare ta aikata mummunar aikin wanda yayi sanadiyar mutuwar sa.

Kamar yadda labari ya zo mana matar wanda ta aikata laifin ta samu ruwan batirin daga wani mai gyaran mota mai suna Kabir.

Makwabta suka yi gaggawar kai mijin asibiti da ke kusa da su amma sai ma'aikatan asibitin suka ki karbansa suka tura su zuwa babban asibitin gwamnatin tarayya da ke nan Zaria.

Bayan an kwantar da shi a asibitin, a ranar 20 ga watan febreru Allah Ya yi masa cikawa.

Rundunar yan sanda na jihar Kaduna sun bayyana cewa sun kama matar tare da Malam Kabir da ya sayar mata da ruwan batir din.

Uwargidan tayi naddamar laifin da ta aikata wa mijin nata wanda ya kai har ga mutuwar shi.

Tana mai cewa "Ina kaunar mijina sosai kuma banyi niyar kashi ba. Nayi bakin cikin jin labari cewa yayi ma aminiyata ciki kuma bai sanar dani ba. Daga majiya na samu wannan labarin.

"Na san na wuce gona da iri amma ina rokon yan uwanshi da yara na har da gwamnati da su yafe mun. Banyi niyar kashi ba" Ta kara.

Rundunar yan sanda sun ce zasu mika su gaban kotu bayan kammala bincike kan lamarin domin fuskantar hukuncin laifin da ta aikata.

Kishi: Wani magidanci ya gamu da fushin uwardakin shi, ta watsa masa ruwan batiri a gaba



CLICK HERE TO READ FULL CONTENT

Brought to you by: RIDBAY | WEBSITE DESIGN & DIGITAL MARKETING